Yusuf Buhari ya kaiwa Gwamnan Bauchi Ta'aziyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi

By Admin

Gwamnan Jihar Bauchi, Abdulkadir Mohammed, ya karɓi Yusuf Buhari, ɗan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Bauchi, a ziyarar ta’aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Ziyarar ta zo ne jin
 kaɗan bayan Yusuf Buhari ya kai ziyara domin yi wa iyalan marigayin ta’aziyya.

 Ya zo tare da tawagar ’yan uwa da abokai, abin da ke nuna cikakkiyar tausayi da goyon baya ga iyalan marigayi da al’ummar Jihar Bauchi baki ɗaya.

Yusuf Buhari ya isar da saƙon ta’aziyyar iyalan Buhari ga Gwamna Bala Mohammed da al’ummar Jihar Bauchi, inda ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban jigo kuma fitaccen jagoran addini, wanda rayuwarsa ta kasance cike da ilimi, tawali’u da hidima ga addinin Musulunci da bil’adama gaba ɗaya. 

Ya jaddada cewa gudummawar da marigayin ya bayar wajen yaɗa ilimin addini da tarbiyya ta wuce ƙarni da iyakokin ƙasa.

A nasa jawabin, Gwamna Bala Mohammed ya nuna godiyarsa bisa ziyarar ta’aziyyar da wannan nuna haɗin kai daga iyalan Buhari.

 Ya bayyana cewa yawan saƙonnin ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan alama ce ta irin girmamawa, tasiri da kuma kyakkyawan tarihin da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bari.

 Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya jikansa, Ya gafarta masa, tare da bai wa iyalansa, mabiyansa da daukacin al’ummar Musulmi haƙuri da ƙarfin zuciya.

Post a Comment

Previous Post Next Post